Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Nijeriya – Akintoye

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙungiyar ƙudirin samar da ‘yancin kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba.

A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60  ciki har da mazauna gida da ‘yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Da ya ke tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Nijeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala.

“Ba kwa jin muryar mu a tituna? ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya.

“Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Nijeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsayin Nijeriya, babu matsala,” inji shi.

By ukarofi