Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Nasarawa a jihar Kano, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da ‘Ogan ɓoye’ ya amince da naɗin mataimaka na musamman guda 60 da za su yi aiki a ɓangarori daban-daban a ƙaramar hukumar.
A cewar takardar amincewa da sakataren ƙaramar hukumar, Ado Muhd Hotoro ya sanya wa hannu, naɗin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da shugaban ƙaramar hukumar ya ke yi na bunƙasa da ayyuka don ci gaban ƙananan hukumomi.
Jerin sunayen waɗanda aka naɗa sun haɗa da masu bayar da rahoto na musamman guda 18 da aka ba su don kula da sassa daban-daban, kasuwanni, da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a cikin ƙaramar hukumar.
Wasiƙar ta kuma ƙara jaddada cewa an yi naɗin ne bisa cancanta, sadaukarwa, gaskiya, da jajircewa, wanda ke nuni da manufar gwamnati na samun ingantaccen shugabanci.
Har ila yau, ta bayyana ƙwarin gwiwar cewa waɗanda aka naɗa za su yi aikin da aka ba su da himma domin tallafa wa manufofin ci gaban ƙananan hukumomin.
