Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar ƙoli ta Shari’a a Nijeriya reshen Jihar Katsina ta gabatar da takardar matsayar ta da ta alummar jihar baki ɗaya ga ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa da suka fito daga Katsina.
Shugaban majalisar ƙoli na Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya jagoranci gabatar da takardun matsayar ga ‘yan majalisar dattijai da na wakilai da suka fito daga Katsina.
Ɗan majalisar wakilai Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya ƙarɓi takardar a madadin ƴan majalisu na ƙasa da ke wakiltar Jihar Katsina.
A jawabin sa bayan ya miƙa takardun matsayar ga Hon Sani Aliyu Ɗanlami, sheik Yakubu Musa Hassan ya yabawa ‘yan majalisun da suka fito daga jihar akan ƙoƙarin da suke na ganin wannan ƙudirin bai sami ƙarɓuwa ba a majalisar.
“Allah ya taimaka duk ɗan majalisar da ke da hannu wajen daƙile dokar sabon harajin da zai jefa al’umma cikin wani yanayi na tsadar rayuwa”inji sheik Yakubu Musa.
Sheik Yakubu Musa Hassan wanda har ila yau shugaban ƙungiyar Izala ne a Jihar Katsina yayi addu’ar “Allah ya yi maganin duk wanda ke nuna goyon bayan sa wajen ganin an aiwatar da dokar da za ta jefa al’umma cikin yanayin tsadar rayuwa”
Shima Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana irin ƙoƙarin da su ke tun lokacin da aka nemi gabatar da ƙudirin a zauren Majalisar dokoki ta ƙasa.
Taron ya sami halartar malamai da shugabannin gamayyar ƙungiyoyin fararan hula ta Jihar Katsina.
A kwanakin baya ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar dokoki ta ƙasa sabon dokar haraji da ya kawo cece-kuce musamman a Arewacin kasar.
