Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa mai son ci gaban matasa ce duba da irin kulawa da yake bai wa cigaban su a fannoni daban-daban.
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Hon Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya bayyana cikar Gwaman Abba Kabir Yusuf shekaru 62 abin farin ciki ne ga matasa da duk al’ummar jihar Kano suna taya shi murna akan wanan ci gaba, da ya shigo da abubuwa na alkhairai a cikin wannan sabuwar shekara.
Ya ce idan aka duba kasafin kuɗi da Gwamna ya gabatar na shekaran nan kusan duk ya bada muhimmanci ga tsare-tsaren matasa na basu tallafi da basu horo akan sana’o’i da bunƙasa iliminsu.
Hon Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano ya ce zasu dage ba dare ba rana wajen riƙa amanar da Gwamna ya ɗora musu na bunƙasa ci gaban matasan jihar Kano.
