Rasuwar matar Sarkin Keffi babban rashi ne ga FMC, cewar Dokta Yahaya Baba

Spread the love

Daga JOHN WADA a Lafiya

Cibiyar samar da magunguna wato Federal Medical Centre (FMC) na gwamnatin tarayya dake birnin Keffi a ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, ta kai wata ziyarar ta’aziyya na musamman wa maimartaba Sarkin Keffi Dokta Shehu Chindo Yamusa da iyalansa bakiɗaya game da rasuwar amaryar sa marigayiya hajiya Maryam Chindo Yamusa wace ta ratsu kwanan nan wato a karshen mako daya gabata.

Ziyarar ta’aziyar daga cibiyar magungunan da suka hada da mahukuntan cibiyar da sauran wakilan su a matakai dabandaban sun ziyarci fadar maimartaba sarkin Keffin ne a karkashin jagorancin babban daraktan cibiyar dokta Yahaya Baba Adamu jimkadan bayan ratsuwar wato ranar Talata na mako da ake ciki.

Dayake jajantawa maimartaba sarkin Keffi dokta Shehu Chindo Yamusa babban daraktan dokta Yahaya Baba Adamu ya bayyana cewa tabbas ba basaraken da masarautar ne kadai suka yi rashin ba harda cibiyar tasu ta kiwon lafiya (FMC) da al’ummar karamar hukumar ta Keffi dama jihar baki daya kasancewar marigayiya matar maimartaba sarki hajiya Maryam Chindo Yamusa ta kasance tamkar uwa ce ga kowa.

Ya bayyana cewa al’ummar garin Keffi da kewayenta baki daya zasu dade suna kewar marigayiyar musamman idan akayi la’akari da gagaruman gudumawa da tayi ta bayar wajen cigaban al’ummar ta musamman mata ‘yan uwan ta dama Keffi baki daya.

Dokta Yahaya Baba Adamu ya kuma yi amfani da damar ta’aziyar inda ya bukaci maimartaba sarkin Keffi alhaji Shehu Chindo Yamusa da iyalan sa dama masarautar Keffi baki daya su rungumi ƙaddarar su kuma fahimci cewa yadda Ubangiji Allah ya kaddara zai faru kenan.

A cewarsa duk da an rasa babban mace mai kima da daraja sosai cikin al’umma amma yakamata koya ya sani cewa Allah yafi son ta ya kuma san dalilin da yasa ya dauki ran ta a wannan lokaci.

Daga nan sai Dokta Yahaya Baba Adamu ya kuma bayyana cewa anata bangaren cibiyar ta samar da magunguna na gwamnatin tarayya dake Keffin za ta cigaba da yiwa marigayiyar addu’a ta musamman don samun ra’amar Ubangiji inda ya yi fatan Allah ya bai wa basaraken da iyalan sa dama masarautar ta Keffi baki daya karfin halin jure wannan babbar rashi da aka yi musamman a wannan lokaci da al’umma ke matukar bukatar gudumawar ta a matsayin ta na uwa ga kowa.

A ƙarshen mako da ake ciki ne dai masarautar ta Keffin ƙan Yamusa mai dinbin tariyi ta sanar da ratsuwar matar ta maimartaba sarki hajiya Maryam Shehu Chindo Yamusa inda tuni akayi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar kana a halin yanzu hukumomi dabandaban ciki harda cibiyar ta samar da magunguna na gwamnatin tarayya dake Keffin itama ta kai nata ziyarar a hukumance.

By ukarofi