Gwamna Abba Kabir ya samu kyakkyawar tarbiyya tun daga gidansu – Muhammad Hussain

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cikar shekaru 62 a Gwamna Abba kabir Yusuf  a rayuwa da cewa masu albarka ne da ba a taba samun Gwamna da ya yi abubuwa na alhairi da yawa cikin dan lokaci da hawansa mulki ba kamarsa.

Alhaji Muhammad Hussain Mashkur daya daga cikin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida a taron da akayi na zuriyar Malam Ibrahim Dabo da akayi a gidan Gwamnati a ranar Asabar.

Ya ce abinda ya jawowa Gwamna ɗabi’antuwa da kyawawan hali saboda irin managarcin tarbiyya ne  daya samu da ga iyayen sa musamman mahaifiyarsa irin  misalin kyakkyawar tarbiyyar sa ce tasa ma da ya miƙe zai je yayi jawabi a taron  zuriyar su sai da ya je ya gaida mahaifiyar sa a inda take zaune.

Alhaji Muhammad Hussain Mashkur ya ƙara da bayyana  cewa  ita mahaifiyar Gwamna Abba Kabir Hajiya Naja’atu mutuniyar kirki ce  wacce ta koyar da shi tarbiyya ta sanin kima da girmama mutane da tausaya musu don haka rayuwar sa take cike da  albarka.

Ya ce irin kariyar Ubangiji da Gwamna Abba Kabir ya ke samu daga makirci na mahassada da maƙiya suke shirya masa sakamakon irin tausayawa da yake wa na kasa ne da son yara.

Muhammad Hussain ya yi nuni da cewa tun kafa  ƙungiyar ake  taron a gidan marigayi ɗan makwayo har yanzu da  Allah ya kawo Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamna  ba a taɓa yin taron kwatankwacin na wannan karon ba da akayi a gidan Gwamnati.

A ƙarshe Alhaji Muhammad Husaini Mashkur ya yi kira ga yan’uwan da abokan arziƙi akan su dage wajen  ci gaba da yiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf fatan alkhairi da addu’oi  akan Allah ya yi riƙo da hannayensa ya gama zangon mulkinsa  lafiya. Su kuma al’ummar jihar Kano gaba ɗaya su alkinta ƙuri’unsu zaɓe mai zuwa su  sake bashi goyon baya  domin ci gaba da ayyuka da yake na bunkasa cigaban jihar Kano da al’ummarta.

By ukarofi