Muna da kyakkyawar jituwa tsakaninmu da Yarabawan Legas – Sarkin Hausawan Festac

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Hausawan Festac, Alhaji Mustapha Musa Katsina ya bayyana cewa, al’ummar Hausawa mazauna Jihar Legas suna ƙara samun jituwa da zaman lafiya tare da fahimtar juna a tsakaninsu da sauran ƙabilu mazauna jihar bakiɗaya.

Sarkin Hausawan wanda kuma shi ne jagaban al’ummar Hausawan Festac ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan da Mai Martaba Sarkin Yarabawan ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin ya kammala naɗa masa rawani tare da jaddada masa sarautarsa ta sarkin Hausawan Festac da kewayenta bakiɗaya.

Taron jaddada naɗin sarautar ya samu halartar waɗansu daga cikin sarakunan Yarabawan ƙaramar hukumar Amuwo Odofin da sauran sarakunan Hausawa na unguwarni daban-daban da ke cikin garin Festac da sauran al’ummar Hausawa bakiɗaya.

Taron ya gudana ne a harabar fadar mai martaba Sarkin Yarabawan garin Muwo Odofin da ke cikin garin Legas.

Tun da farkon taron dai kafin jaddada wa Sarkin Hausawan na garin Festac Alhaji Mustapha Musa rawanin sarautarsa ta Sarkin Hausawan Festac, sai da sarkin Yarabawan ya umarci sakataren fadarsa ya miƙe tsaye ya karanto wa al’ummar da suka zo taron dalilan da suka sanya sarkin Yarabawan ya jaddada wa Alhaji Mustapha Musa wannan sarautar tasa ta Sarkin Hausawan Festac.

Sakataren fadar sarkin Yarabawan ya cigaba da cewa, dalilan kuwa su ne  kyawawan halayensa nagari waɗanda suka haɗa da sanin dokokin halin zamantakewar ɗan adam da ƙoƙarinsa na haɗa kawunan al’umma domin su cigaba da zaman lafiya tare da sanin ya kamata da sauran kyawawan halayensa makamantan irin waɗannan.

Ya ce, haka kuma a wani ɓangare ya samu shaida a wurare daban-daban ta fannin rayuwarsa. 

Sarkin Yarabawan ya yi jawabin huɗuba ga Sarkin Hausawan Alhaji Mustapha Musa Katsina, inda bayan ya kammala taya sarkin Hausawan murnar samun wannan sarauta.

Ya cigaba da shawartarsa da ya ƙara ƙoƙari a wajan gudanar da irin waɗannan halaye nasa nagari.

Hakazalika, Sarkin Hausawan na Festac, Alhaji Mustapha Musa Katsina shi ma ya yi jawabin godiya ga fadar sarkin Yarabawan, inda ya ce yana mai matuƙar nuna farin cikinsa dangane da samun wannan sarauta ta shi, yana fatan Allah ubangiji ya yi masa jagoranci bisa kan ƙamari kuma zai yi iyakar ƙoƙarinsa wajen kare mutuncin al’ummar Hausawan Festac bakiɗaya.

By ukarofi