
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce zai jagoranci yi wa ɗan majalisarsu na tarayya, Hon. Ali Sani Madakin Gini kiranye daga Majalisar, sakamakon al’ummar ƙaramar hukumar Dala da Kano ba sa buƙatar wakilcinsa.
Kwamared Waiya ya bayyana haka ne a yayin taron masu-ruwa-da-tsak na karamar hukumar Dala da ƴan jamiyyar NNPP, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Mumbayya dake Kano.
Ya ce ƙaramar Hukumar Dala tana buƙatar jagora jajirtacce wanda zai kai matsalolin al’ummar yankin Majalisar Wakilai domin a magance su.
Kazalika, Waiya ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa tarin muƙaman da ya bai wa waɗanda suka fito daga ƙaramar hukumar.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar NNPP na Dala da sauran masu-ruwa-da-tsaki na tafiyar Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar.
