Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A taron da ya gudana a Katsina na miƙa tuta ga ƴan takarar shugabancin ƙananan hukumomi a jihar an jiwo gwamnan a jawabin da ya gabatar yana ta ambaton jam’iyyar PDP maimakon jam’iyyar APC wanda haka yayi ta jawo kace nace musamman daga bakin yan adawa.
Wannan ya sanya jam’iyyar adawa ta PDP ta fitar da wata sanarwar inda take yabawa gwamnan da ya fito da bakin sa ya tabbatar da cewa Jihar Katsina jiha ce ta PDP.
To sai dai mai magana da yawun gwamna Muhammad Kaula ya bayyana suɓul da bakan da cewa hakan yana nuna cewa Dikko Raɗɗa ɗan Adam ne kamar kowa.
“Dikko Raɗɗa ɗan Adam ne kamar kowa yana iya kuskure kamar yadda kowa keyi ba akan sa aka fara ba” inji Kaula.
Ya bada misalin Firaministan Birtaniya, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar labour duk sunyi irin wannan suɓul da baka.
Kaula yace gwamna Dikko Raɗɗa yanzu ya maida hankali sa ne kan yadda jam’iyyar sa ta APC za ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 34 da zai gudana a tsakiyar watan gobe.
Gwamna Dikko Raɗɗa sai ya yi kira ga ya’yan jam’iyyar APC a Jihar Katsina da su cigaba da sadaukar da kai tare da bada tasu gudunmawa wajen cigaban jihar, kada su bari abinda bai kai ya kawo ba ya zama abin magana.
