2027: Ba na adawa da haɗakar jami’iyyu, inji Peter Obi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai na cewa yana adawa da haɗakar jami’iyyun siyasa don kayar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Idan za a iya tunawa, a yayin wani taron ƙasa na kwanaki biyu kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya a ranar Litinin, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ba zai shiga cikin duk wani haɗaka da ke da manufar “karkatar da madafun iko ba”.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Tuwita a ranar Talata, Obi ya fayyace kalaman nasa na farko, inda ya ce kafafen yaɗa labarai da dama sun yi masa gurguwar fahimta, don haka suka rinƙa ƙirƙiro labarin ƙarya game da matsayinsa.

Ya ce: “Na lura cewa hirar da na yi ta gaskiya a jiya, kafafen yaɗa labarai da yawa sun yi kuskure wajen yaɗa maganar, inda suka haifar da wani labari na ƙarya da ya ɓata matsayina.

“Bari in saita komai. Ni ba na adawa da haɗaka. A gaskiya ni ina sonta, ba wai don neman mulki ba, sai dai in ɗora Nijeriya a kan hanyar ɗaukaka.

“Ba zan taɓa bayar da shawarwari ga duk wani ƙawance ko haɗaka da ba zai fifita jin daɗi da ci gaban talakawan Nijeriya ba.

A cewarsa, dole ne shugabanci ya kasance akan hanyar hidimta wa al’umma, ba son rai ba, amma yana buƙatar kowa ya canja tunaninsa game da mulki.

By ukarofi