Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dan majalisar da ke wakiltar Kudancin Kaduna, Sanata Sunday Marshall Katung, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda hare-hare da kashe-kashe da kuma sace-sacen jama’a suka sake kunno kai a wasu sassan kudancin jihar. Ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya yi Alla-wadai da ayyukan ‘yan ta’adda a ƙananan hukumomin Kauru, Kachia, Zangon Kataf, Kaura, da Sanga, yana mai cewa tashe-tashen hankulan ya haifar da “mummunan zafi, wahala da ba za a taɓa mantawa da su ba, tare da girgiza rayuwar al’ummarmu.”
Ya ci gaba da cewa, “A kwanakin baya ne ‘yan bindigan suka yi garkuwa da wasu mutanen yankin 22, galibinsu mata da ƙananan yara, a wasu hare-hare da suka kai a yankin Kugauta da ke Kusheka, kuma masarautar Kumana, da kuma al’ummar Kitanda na Geshere, masarautar Kumana a karamar hukumar Kauru.”
Ya kuma bayyana hare-haren a matsayin “sabon cin fuska ga al’ummar Kudancin Kaduna masu son zaman lafiya,” ya ƙara da cewa bai kamata a ci gaba da gudanar da irin wannan ta’asa ba am daƙile masu aikatata ba.
“Bai kamata a ci gaba da wannan ta’asa da ake yi wa mutanenmu ba. Kuma dole ne a daina yanzu,” inji shi.
Sanatan ya jaddada ƙudirinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ya yi misali da sashe na 14 (2) (b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, wanda ya bai wa gwamnati fifiko kan tsaro da jin daɗin ‘yan ƙasa.
“Tun daga nan na ba da fifiko kan tsaron kowane ɗan ƙasa. Don cimma wannan burin, ina bayar da cikakken haɗin kai da gwamnatin jihar Kaduna da kuma babban hafsan tsaro don tabbatar da kafa rundunar Operation Base (FOB) a ƙaramar hukumar Kauru da sauran al’ummomi domin tunkarar maharan,” inji shi.
Ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi, ya kuma buƙace su da su ƙara ƙaimi domin daƙile hare-haren.
“Yayin da nake godiya ga jajirtattun jami’an tsaronmu maza da mata na jami’an tsaronmu kan ƙoƙarin da suke yi na ganin an shawo kan matsalar, ina roƙon su da su ruɓanya ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a Kudancin Kaduna, Jihar Kaduna, da Nijeriya a matsayinsu na ƙasa baki ɗaya,” inji shi.
Sanata Katung ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar samar da bayanan sirri da za su kai ga cafke maharan da masu ba su bayanai.
