Hukumar Tafkin Chadi ta fayyace batun ficewar Nijar daga MNJTF

Spread the love

Daga MAHDI MISA MUHAMMAD

Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Tafkin Chadi kuma shugaban tawagar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF), Amb. Mamman Nuhu, ya fayyace matsayin Jamhuriyar Nijar a halin yanzu a haɗin gwiwar sojojin yankin, inda ya bayyana cewa ƙasar ba ta janye gaba ɗaya ba.

Nuhu ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Laraba, jim kaɗan bayan buɗe taron ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi karo na 5.

“Nijar ba ta janye gaba ɗaya daga rundunar ta MNJTF ba. Ba gaskiya ba ne Nijar ta tafi. Nijar ba ta fita ba,” inji shi.

Ya ce a baya-bayan nan sojojin Nijar sun shiga cikin hare-hare daban-daban guda huɗu da MNJTF ta yi na yaƙi da Boko Haram da kuma ISWAP.

Tun da farko a jawabinsa na buɗe taron da ya samu halartar gwamnonin ƙasashen yankin tafkin Chadi da suka haɗa da Kamaru, Nijeriya, Chadi, da Nijar, Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS) Janar Christopher Musa ya yi kira ga sojojin Nijar da kada su janye daga rundunar ta MNJTF.

“Mu iyali ɗaya ne. Babu wata taƙaddama da ba za mu iya warwarewa ba,” inji shi.

Hedikwatar MNJTF tana N’Djamena, babban birnin ƙasar Chadi. Kamaru, Chadi, da Nijar makwabta ne na Nijeriya.

By ukarofi