
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta biya manoma 150 diyyar gonakinsu da gwamnati ta amsa domin gina Jami’ar Koyon Aikin Noma a Funtua.
Kwamishinan Ƙasa da Sufayo na jihar, Dakta Faisal Umar Kaita ya ƙaddamar da bada cakin kuɗin a madadin Gwamna Dikko Raɗɗa.
Ya ce “ba za a taɓa wuri ba har sai an biya diyya. Hakan ne ya kawo jinkirin fara biyan su.”
A jawabinsa a wajen taron shugabannin kwamitin TETFUND na Majalisar Dattijai, Sanata Muntari Ɗan Dutse ya ce sai da aka kai ruwa rana kafin samun amincewar Shugaba Bola Tinubu na ganin an samar da jami’ar a Funtua.
Ɗan Dutse, wanda shi ke wakiltar yankin Funtua ya jinjina wa al’ummar yankin bisa haƙuri da suka nuna kafin samun wata makaranta na gaba da sakandare a Funtua, “..gashi hakuri da kuka nuna ya yi rana “inji Sanatan.
Ya ƙara da cewa, kammala aikin gina jami’ar zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin yankin domin mutane daga sassa daban-daban za su riƙa zuwa karatu a jami’ar.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua, Alhaji Mannir Suleiman, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa da Sanata Ɗan Dutse bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da samuwar jami’ar.
Ya ce ganin cewa mafi yawan mutanen yankin manoma ne, jami’ar za ta taimaka wa matasan yankin wajen samun ilimin sabbin dabarun noman zamani da zai amfani al’ummar jihar da ƙasa baki ɗaya.
Malam Suleiman ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki da sauran al’ummar yankin da su bada tasu gudummawar na ganin jami’ar ta tsaya da ƙafafunta.
