An kama ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Belgium Radja Nainggolan a wani ɓangare na bincike kan safarar hodar iblis.
Dan wasan mai shekaru 36, yana ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ’yan sandan Belgium ne suka kama a safiyar ranar Litinin, bayan wasu samame daban-daban da aka kai a faɗin ƙasar.
“Binciken ya shafi bayanan da ake zargin an shigo da hodar iblis daga Kudancin Amurka zuwa Turai, ta tashar ruwa ta Antwerp, da kuma sake rarraba shi a Belgium,” inji ofishin mai gabatar da ƙara na Brussels a cikin wata sanarwa.
Babu wani ƙarin bayani da aka bayar ga jama’a.
Kamen dai na zuwa ne kwanaki shida kacal bayan da Nainggolan ya dawo daga ritaya ya kuma koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Lokeren a rukunin na biyu na gasar Belgium.
Ya zura ƙwallo a wasansa na farko, inda ya bai wa ƙungiyarsa maki a wasan da suka tashi 1-1 gida da K. Lierse.
Dan wasan tsakiyan ya shafe yawancin rayuwarsa a Italiya, inda ya taka leda a Roma da Inter Milan. Tsakanin 2009 da 2018, ya buga wasanni 30 a tawagar ƙasar Belgium
