Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu
Tsohon mashawarci na musamman ga Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, kan harkokin bunƙasa ilimin firamare da sakandire, Hon. Isa Bamalum Bashir Gashu’a (Bombay) ya bayyana Gwamnan a matsayin wanda ya farfaɗo da matasan jihar tare da yi musu goma ta arziki ta hanyar ba su cikakkiyar damar a dama dasu a kowane fannin gudanar da gwamnati a jihar.
Hon. Bamalum ya bayyana hakan ne a sa’ilin da yake fira da MANHAJA, ranar Jummu’ar da ta gabata, inda ya ƙara da cewa, wannan matakin da Gwamna ya ɗauka ya kawowa jihar ci gaba tare da baiwa matasa damar baje kolin fasaha da ilimin da Allah ya hore musu wajen gina jihar Yobe. Saɓanin gwamnatocin baya waɗanda suka yi wa tafiyar matasa shakulatin ɓangaro.
“Ko shakka babu Maigirma Gwamna Buni ya cancanci mu yaba masa tare da bayyana shi a matsayin jagora nagari mai kishin matasa, mai kishin ci gaban al’ummar jihar Yobe baki ɗaya. Ya baiwa matasa damammaki don su alkinta kwarewarsu da kuma taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’ummar jihar Yobe.
“Sannan kuma waɗannan matasa da aka damƙa wannan nauyi a hannun su, ba kawai suna amfani da ita don gina kansu kawai ba, a’a, suna amfani da wannan damar wajen taimakawa da ƙarfafa sauran matasa domin su ma su samu nasara a rayuwa- domin cimma kyawawan manufofin Gwamna Buni,” inji shi.
Isa Bamalum ya ƙara da cewa, waɗannan matasan da Gwamna Buni ya zaƙolo don bayar da tasu gudunmawar ciyar da jihar Yobe gaba; ba yan jeka-na-yika bane, ƙwararru ne waɗanda suka sahara kuma suke bayar da gudunmawa a fannin ci gaban al’umma, kuma wasunsu Farfesoshi ne, wasu daktoci ne. Irinsu Dr. Abubakar Kagu, Dr. Mohammad Goje, Malam Abdullah Bego, Dr. Sharif Almuhajir, Dr. Ibrahim Ali Abbas, Malam Hashim Nuhu Hashim da makamantan su.
“Misali a wannan yanki namu na Yobe ta Arewa, mu na alfahari da ƙoƙarin da waɗannan jagororin matasa suke yi; musamman Malam Hashimu Nuhu Hashim, Mailambu, saboda irin rawar da yake takawa wajen ganin cewa matasan jihar Yobe sun tsayu da kafafunsu, wannan ba ƙaramin abin a yaba ba ne.
“Ta dalilin Malam Nuhu Hashim, matasa da dama sun samu aikin gwamnati, wasu da dama sun samu jarin sana’a tare da talkafin noma, wasu kuma da sama sun mallaki filaye da gidajen da zasu zauna. Duka wannan ya samu ne albarkacin shi Maigirma Gwamna Buni.”
Har wala yau, ya ce a shirye matasan jihar Yobe suke wajen bayar da kowane irin gudunmawa don ganin jihar ta ci gaba, inda kuma ya bukaci Gwamna Buni ya ci gaba da baiwa matasa irin su Nuhu Hashim Mailambu dama a matsayinsa na amintaccen mutum.
A hannu guda kuma, Hon. Bamalum ya yi tsokaci dangane da ƙorafin da Gwamnan jihar yake yin kan rashin tallata ayyukan da yake yiwa al’ummar jihar Yobe, inda ya ce ko shakka babu wasu yan siyasa da masu riƙe da manyan madafun iko ba su damu da ci gaban jihar ba, face kawai kansu suka sani.
“Ko shakka babu wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati ba su da kishin jihar Yobe a zukatansu balle su tallata ayyukan da gwamnatin jihar Yobe ta sanarwa da jama’a, don a yaba wa Maigirma Gwamna Buni, alhali ya na su amana, face kawai suna amfani ofisoshin su wajen baiwa yaran su yan social media kuɗi su tallatasu, saɓanin ayyukan gwamnati.
“Saboda haka, mu na kira ga Maigirma Gwamna ya murza gashin baki ya ɗauki matakan da suka dace tun lokaci bai ƙure ba, wajen takawa duk wani jami’in gwamnati birki, ko shi waye idan ba zai bi manufofin gwamnati ba. Ya sake duba waɗanda ya dace ya damƙa musu amana a yankunansu.
“Saboda wallahi wasu daga cikin waɗanda ya ɗauka a matsayin amintattun da ya yarda dasu ba da gaske suke ba, kuma basu damu da ci gaban al’ummar su ba ballantana ci gaban gwamnatin jihar Yobe ba. Kansu da yayansu kawai suka sani, kuma idan an ci gaba a haka to za a samu matsala,” ya nanata.
Hon. Isa Bamalum Bashir ya ƙara da cewa, a kwanan baya Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umurnin cewa masu ruwa da tsaki (Stakeholders) su aiwatar da mayar da dukkan SSA, SA; banda waɗanda suka rasu ko suka sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya. Amma waɗannan masu yiwa tafiyar Gwamna ƙafar-ungulu ba su aiwatar ba, saɓanin haka sai suka rinƙa sanya yaransu tare da cire sunayen waɗanda ba sa ƙauna.
