2025: CBO Veronica Abah ta buƙaci ƙarin haɗin kai daga kwastomomin AEDC

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugabar sashin harkokin kasuwanci wato Chief Business Officer a turance na kamfanin wutar lantarki da ake kira Abuja Electricity Distribution Company (AEDC), Veronica Attama Abah ta taya abokan hulɗan kamfanin wutar lantarki baki ɗaya murnar ganin sabuwar shekarar 2025 da ake ciki, inda ta ce kamfanin zai cigaba da inganta harkokin kasuwancin samar wa ɗimbin kwastomomin nasu bakiɗaya wutar lantarkin.

CBO Venonica Attama Abah ta bayyana haka ne a cikin wani sakon sabuwar shekarar 2025 da aka raba wa manema labarai ranar Laraba na mako da ake ciki wadda wakilin mu ya samu kwafi.

Ta yaba wa ɗimbin kwastomomin nasu waɗanda ke amfani da wutar lantarkin ta Abuja Distribution Company baki ɗaya dangane da haɗin kai da kyakkyawar dangantakar kasuwanci dake tsakanin su biyun, inda ta ce tuni hukumar kamfanin samar da wutar lantarkin ta yanke shawarar cigaba da yin duka mai yiwuwa wajen ganin kwastomomin nasu suna cigaba da samun wadatacciyar wutar lantarki a wannan sabuwar shekarar ta 2025 kamar yadda take yi inda ta buƙaci duka kwastomomin su cigaba da wannan haɗin kai da suke ba su.

Shugabar shashin na kasuwanci a hukumar samar da wutar lantarkin CBO Veronica Attama Atah ta kuma yi amfani da damar inda ta bayyana cewa ƙofofinta a buɗe suke a kullum wa duk wani ko wata kwastomar kamfani dake da wani damuwa ko wani ƙorafi na daban akan yanayin hulɗa da kamfani don su je su bayyana damuwarsu ɗin inda ta tabbatar cewa kamfanin ba zai  ɓata lokaci ba wajen tabbatar ta warware matsalar.

Veronica Attama Abah ta kara da cewa duk da cewa a duk harkokin kasuwanci irin wannan tsakanin hukumar da kwastomominta a wasu lokutan ba a rasa rashin jituwa da saɓani amma yana da kyau idan hakan ya faru a riƙa zaunawa tare a tattauna don samun mafita maimakon a riƙa ɗaukar doka a hannu wadda ta ce hakan sam bai dace ba.

Har ila yau CBO ɓeronica ta ƙara da cewa kawo yanzu al’ummomi da ƙungiyoyi da hukumomi masu zaman kansu dama na gwamnati a duka matakai dake wannan kasuwancin wutar lantarki da kamfanin na cigaba da yaba musu game da inganci da kuma aiki tuƙuru da suke yi don tabbatar ana cigaba da samar musu da ingantaccen wutar lantarkin ɗin inda ta ce hakan ne ma ya sa kamfanin yake cigaba da iya ƙoƙarin shi don tabbatar da kyakkyawar sunar.

Daga nan sai ta sanar cewa duk wadda ke da sha’awar kasuwancin wutar lantarki da hukumar zai iya ziyartar ofishoshin su dake sassan Abuja da jihar Nasarawa da sauran jihohin kasar nan dabandaban kana ta kuma yi amfani da damar inda ta shawarci kwastomomin nasu su rika tuntubar ainihin hukumar ta AEDC maimakon bin ta wasu ma’aikatan wutan lantarkin na boge wadanda basu kware ba basu kuma san kan aikin ba kana daga baya su samu matsalar da wutan lantarki a gidajen su ko wuraran aikin su da sauran su.

Wakilinmu dai bayan ganawa na musasmman da ya yi da wasu kwastotomin kamfanin AEDC ɗin ya gano cewa a yanzu haka al’ummar yankin Abuja zuwa garin Keffi a jihar Nasarawa da kewayensu suna cigaba da yaba wa hukumar samar da wutar lantarkin musamman shashin kasuwancin a ƙarƙashin jagoracin CBO Veronica Attama Abah game da ingantacciyar da kuma wadatacciyar wutar lantarki da suke samu akai-akai tun a bara har zuwa wannan sabuwar shekarar ta 2025 kana suka kuma buƙaci kamfanin ya cigaba da hakan.

By ukarofi