NAFDAC ta rufe kamfanonin samar da jabun madara da Coca-Cola a Abia

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta rufe babbar kasuwar maƙabarta da ke garin Aba, jihar Abia, a karo na biyu cikin shekaru biyu.

Hukumar ta ce, ta bankaɗo tare da kwace kayan abinci da abubuwan sha na jabu da marasa inganci da kuɗinsu ya haura Naira Biliyan 5 a wani aiki na baya-bayan nan mai taken ‘Operation Clean Up Aba’.

Kasuwar Maƙabartar ta yi ƙaurin suna wajen samar da kayan sha na jabu, abubuwan sha, da kayan abinci na jabu, wanda aka bayyana a matsayin cibiya mafi girma a Afirka ta barauniyar giya da abin sha.

Darakta-Janar na Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, a cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu a ranar Talata, ta bayyana harin a matsayin “matakin da ya fi ɗaukar hankali a tarihin kasuwar.”

“Wannan wani babban mataki ne na kiyaye lafiyar jama’a da kuma daƙile yaɗuwar kayayyakin jabu a Nijeriya,” inji Adeyeye.

A yayin aikin, an gano sama da masana’antu na wucin gadi 240, waɗanda ke samar da jabun kayayyaki a cikin rashin tsafta.

Adeyeye ya bayyana cewa, waɗannan masana’antun sun yi amfani da sinadarai masu cutarwa, gurɓatacciyar ruwa da kuma kwalabe da aka sake sarrafa su wajen ƙera nau’ukan jabu na shahararru irin su Hennessy, Seaman Schnapps, Coca-Cola, Sprite, Peak Milk da Hollandia Yoghurt.

“Waɗannan abubuwa masu laifi suna amfani da tushen ruwa marasa tsafta, saccharin, abubuwan canza launi, da sinadarai masu cutarwa waɗanda ba su dace da amfani da ɗan adam ba. Yin lalata da abubuwan sha ya haɗa da sikari da sitaci mai rahusa maimakon ‘ya’yan itace ko inabi,” inji Adeyeye.

Ta ƙara da cewa, sama da katan 1,500 na kayayyakin jabu ne aka lalata a wurin, inda aka kiyasta kuɗin titinan kayayyakin da aka kama da kuma lalata su ya kai Naira biliyan 5.

Ta ce, aikin ya kuma kai ga gano wasu rumbunan ajiya guda uku da aka ajiye na Hollandia Yoghurt da ya kare domin a gyara su a ranar 22 ga watan Janairu.

Hukumar NAFDAC ta yaba wa gwamnatin jihar Abia ƙarƙashin jagorancin gwamna Aleɗ Otti bisa goyon bayan wannan samamen.

“Taimakon Gwamna Aleɗ Otti, Magajin Garin Aba ta Kudu, da kwamitin riko na kasuwar ya kasance mai matuƙar muhimmanci ga nasarar Operation Clean Up Aba,” inji Darakta Janar.

Hukumar ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su sanya ido sosai tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin NAFDAC mafi kusa.

“Mun ƙuduri aniyar kare lafiyar al’umma tare da kawar da kasuwannin jabu da kayayyaki marasa inganci,” inji Adeyeye.

By ukarofi