Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu kimanin Naira Biliyan 2.4 a shekarar 2024 daga yarjejeniyar aure ta hanyar rajistar aure a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida.
Olubunmi Tunji-Ojo, Ministan Harkokin Cikin Gida ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wata tattaunawa da manema labarai.
Ministan ya ce, ma’aikatar ta kuma samu sama da Naira Biliyan 3 da miliyan 200 daga aikace-aikacen rabon kason jama’a, inda ya ce gaba ɗaya an samu ƙaruwar kashi 150 cikin 100 na kuɗaɗen shiga.
Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta maido da baƙi 828 zuwa ƙasashensu daban-daban a shekarar 2024.
Duk da dai bayyana takamaiman laifukan da suka aikata ba, ya ce Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ce ta mayar da su gida.
