Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Duk da cewa ƙasashen biyu suna da nisan kilomita 11,472, amma manufar taimakon ƙasashen waje ta Amurka ta yi matuƙar tasiri ga Nijeriya, inda aka kashe maƙudan kuɗaɗe da suka kai Dala Biliyan 1.16 a shekarar 2022, da kuma dala miliyan 767 a shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da kusan dukkanin tallafin kuɗaɗe na shirye-shiryen taimakon ƙasashen waje, ban da ƙawayenta Isra’ila da Masar. Umurnin daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a ƙarshen mako kuma ya haɗa da keɓancewa ga shirye-shiryen abinci na gaggawa, amma ba shirye-shiryen kiwon lafiya waɗanda magoya bayansu suka ce suna ba da muhimman ayyuka na ceton rai ba a duniya.
ƙungiyoyin agaji sun bayyana kaɗuwarsu da umarnin, inda suka bayyana fargabar cewa hakan na iya haifar da rashin zaman lafiya da asarar rayuka a duniya.
Idan tallafin ya tsaya, Nijeriya za ta buƙaci ta binciko wasu hanyoyin da za ta toshe ramuka da asusun bayar da tallafin ke haifarwa, wanda zai iya haɗawa da karɓar rance wanda hakan zai iya ƙara yawan basussukan ƙasar.
A halin yanzu, miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke fama da cututtuka daban-daban, kuma suka dogara da taimakon Amurka na fuskantar makoma mara tabbas. Wannan janye tallafi yana da yiwuwar kawo cikas ga muhimman tsare-tsare na kiwon lafiya, da ci gaban tattalin arziki, da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin tsaro da ke da muhimmanci ga ci gaban Nijeriya.
A kodayaushe Nijeriya na daga cikin ƙasashe takwas da ke kan gaba wajen karɓar taimako daga Amurka. Wani rahoto da aka bayar a shekarar 2024 a wani ɓangare na taimakon ƙasashen waje ya nuna cewa Nijeriya ta samu tallafin dala miliyan 370 a fannin kiwon lafiya; Dala miliyan 310 na taimakon jin ƙai; Dala miliyan 35 sun shiga kuɗin gudanarwa; dala miliyan 24 akan ilimi; noma ya samu dalar Amurka miliyan 7.8 sannan an kashe dala 7.4 akan wasu matsalolin a bara.
