Cikakken bayani kan takardun inshorar mota don guje wa faɗa wa matsala da ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tuƙi abu ne da ba ka iya hasashensa abin da zai faru a kodayaushe ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci kana iya samun matsala a lokacin da ka ke yin sa cikin nishaɗi.

Matsalar kuma ka iya zama karo ne aka yi da wani abin hawa wanda a wani lokaci ya kan zama babba ko ƙarami la’akari da yadda ya zo.

A wasu lokutan akan samu raunuka da har sukan kai ga zuwa asibiti wanda a nan ana buƙatar amfanin inshora da ake kira da ‘third party insurance’.

Baya ga kiyaye doka ga matuƙan da suka mallaki inshorar, hakan kuma zai taimaka wajen doka ta ɗauke nauyin kula da waɗanda suka raunata daga hatsarin da ka yi sababinsa.

Adadin waɗanda suke da takardun bogi na inshora a Nijeriya ya kai miliyan 9.4 sakamakon mallaka daga wakilan bogi ga matuƙa.

Ƙungiyar masu inshora ta Ƙasa ta ce motoci miliyan 2.72 ne kaɗai suke da takardun inshora na ƙwarai a zuwa watan Fabrairun 2021.

A Disambar 2022 ne Gwamnatin Tarayya ta ofishin Hukumar Kula da Harkokin Inshora (NAICOM), ta yi gyara ga farashin inshorar motoci wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Junairun 2023.

A gyaran da aka yi kamar yadda News Point Nigeria ta wallafa, motocin gida da ke biyan N5,00 ga N1m na TPPD, yanzu za su riƙa biyan N15,000 ga N3m na TPPD.

Haka kuma motocin da ake kasuwanci da su zasu riƙa biyan N100,000 ga N5m na TPPD, sai masu adaidata sahu – N5,000 ga N2m na TPPD, sai kuma babura N3,000 ga N1m na TPPD.

Za a iya ziyartar wannan shafin don neman ƙarin bayani; www.askniid.org, ko kuma a aika saƙo ta 56511#.

By Babaji