
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano yi ƙaddamar da shugabanni da kwamishinoni da mambobin hukumomin Shari’a da Zakka.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya bayyana yadda Kano ta kasance cibiyar addinin Musulunci ganin yadda ta ke da sanannun malamai, makarantun islamiyya da cibiyoyin nazarin addinin Musulunci.
Ya ce an naɗa waɗanda aka bai wa muƙaman ne bisa cancanta inda hakan zai taimaka wajen sauke nauye-nauyensu bisa gaskiya da adalci.
Gwamnan ya yi kira ga Hukumar Shari’a da ta tabbatar da haɗin kan al’ummar musulmi daga ɓangarori daban-daban don bunƙasa zaman lafiya da ci-gaban tattali a jihar.
Haka kuma ya nemi Hukumar Zakka da ta samar da tsari mai kyau wajen tattara kuɗaɗen Zakka daga masu kuɗi don taimakon marasa galihu wanda hakan zai taimaka wajen rage raɗaɗin talauci acikin al’umma.
Ga jaddawalin waɗanda aka naɗa a hukumomin:
Hukumar Shari’a
- Shugaba: Sheikh Abbas Abubakar Daneji
- Babban Kwamishina na I: Malam Yahaya Gwani Hadi
- Babban Kwamishina na II: Sheikh Ali Dan Abba
- Mambobi:
- Malam Abubakar Mai Ashafa
- Malam Naziru Saminu Dorayi
- Sheikh Mukhtar Mama
- Sheikh Ibrahim Inuwa
- Malam Adamu Ibrahim
- Alhaji Abubakar Sharif Bala
- Alhaji Yawale Suleiman Gulu
- Malam Aliyu Umar
- Alhaji Muhammad Kabir Na’bi
- Malam Nasiru Sheikh Aliyu Harazimi
- Sakatare: Sheikh Dr. Sani Ashir
Hukumar Zakkat da Hubusi
- Shugaba: Barrister Habibu Dan Almajiri
- Babban Kwamishina na I: Sheikh Nafi’u Umar Harazimi
- Babban Kwamishina na II: Dr. Ali Quraish
- Mambobi:
- Malam Yahaya Muhammad Kwana Hudu
- Sheikh Hassan Sani Kafinga
- Sheikh Arabi Tudun Nufawa
- Malam Sani Sharif Umar
- Farfesa Garba Muhammadu Tofa
- Malam Adamu Muhammadu Andawo
- Malam Surajo Usman
- Sheikh Adamu Guda
- Malam Inuwa Mustapha
- Malam Nura Badamasi
- Malam Abdullahi Sarkin Sharifai
- Wakili daga Hukumar Kula da Ma’aikatan Kano
Gwamna Abba ya kuma ce yana sa rana sabbin jami’an za su gudanar da ayyukansu bisa ƙwarewa da kuma taimaka wa jagorancin musulunci a jihar.
