Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Hukumar Alhazai ta ƙasa ta ba Jihar jigawa kason kujeru 1809 a matsayin kujerun da za a sayarwa maniyyatan da suke da sha’awar sauke farali a wannan shekarar.
Shugaban hukumar alhazai ta Jihar Jigawa Malam Umar Ahmed Labbo shine ya sanar da haka a wani taron manema labarai da hukumar alhazan ta Jihar jigawa ta kira a yau ɗin nan.
Babban darakta na hukumar Malam Ahmed Umar Labbo yace gwamnatin Jihar Jigawa ta rantawa hukumar alhazai ta Jihar Jigawa Naira biliyan uku da naira Miliyan 360 a matsayin wani kuɗin bashi da hukumar za tayi amfani da su domin kare kujerun da hukumar alhazai ta ƙasa ta baiwa Jihar ta Jigawa.
Ya ƙara da cewar a matakin jiha sun raba kujerun da a ka basu zuwa ƙananan hukumomin jihar 27 kuma ƙaramar hukumar da tafi ƙwazo wajen sayar da kujeru itace tafi samun kujeru masu yawa domin sayar wa alhazan da suke da buƙata .
Saboda hakane ma hukumar ta Kirayi taron masu ruwa da tsaki na jami anta da ke ɗaukacin ƙananan hukumomin Jihar 27 aka shirya masu bita akan aikin hajjin na bana tare da faɗakar da su makamar aiki akan dokokin aikin hajjin na bana .
Ya ƙara da cewar za a ci gaba da amsar kuɗaɗen kujerun alhazai adadin jihar dan ganin an ƙara sa sauran kujerun da suka rage ba a sayar ba.
Yace sun ɗauki matakin hakane domin ganin an biya gwamnatin tarayya kuɗaɗen kujerun da aka basu akan lokaci kamar yadda yake a dokance.
Wajen batun wurin kwana kuwa yace hukumar alhazai ta jihar Jigawa ta kamawa maniyyatan jihar masauki a kusa da harami da nufin sauƙaƙa wa maniyyata yayin da akayi yarjejeniya da kamfanonin ciyar da maniyyata abinci sau uku a rana da nufin kyautatawa mahajjanta.
