
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Hukumar tsaro ta Civil Defense (NSCDC) reshen jihar Zamfara ta jajenta wa iyalan waɗanda gobarar makarantar allo ta shafa a ƙaramar hukumar Ƙauran-Namoda da ta yi sanadin mutuwar almajirai 17.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin kwamandan jihar, CC Sani Mustapha sun kai ziyarar jaje ga Mai Martaba Sarkin Ƙauran-Namoda, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha, Shugaban Karamar Hukumar, Alh. Munnir Mu’azu Haidara da waɗanda lamarin ya rutsa da su.
A ranar Larabar da ta gabata ne wata gobara ta laƙume rayukan dalibai almajirai 17 yayin da aka ceto wasu goma 17 da suka samu munanan raunuka.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba duk da cewa rundunar ta NSCDC ta gano wata alamu da ake zargin ita ce tushenta yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.

A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar a Jihar, ASCII Umar, Mohammad M., a wata sanarwa da ya fitar, ya ce kwamandan rundunar Sani Mustapha ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.
“Muna baƙin ciki tare da ku, muna kuma rokon Allah Ya jikan su da rahama.”
Kwamandan ya roƙi al’umma da su tabbatar da fitar da itacen wuta ko gawayi da na’urorin dafa abinci na lantarki bayan an yi amfani da su domin taƙaita abubuwan da ka iya faruwa a nan gaba.
Rundunar ta kuma bayar da tallafin kuɗi don rage nauyin kuɗaɗen jinyar waɗanda abin ya shafa da kuɗi N100,000.
A nasa jawabin, Munnir Mu’azu Haidara, ya yaba wa kwamandan bisa wannan karamcin da ya nuna tare da sauran jami’an rundunar.
Mai Martaba Sarkin Ƙauran-Namoda, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha ya jinjina wa NSCDC bisa namijin ƙoƙarinsu na samar da zaman lafiya a yankin.
