Manufar ‘Kano Proper’ shi ne tabbatar da ƙudirin gwamnati na ci gaban al’umma sun kai gaci – Mailemo

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa Kano Proper na daga cikin durkoki guda biyar na tsarin Kwankwasiyya da aka ƙirƙiro tun zamanin jagoran Kwankwasiya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso yake gwamnan jihar Kano domin sa ido da tabbatar da nasarar aiwatar da ayyukan da ake gudanarwa.

Shugaban ‘Kano Proper’ Hon. Habibu Saleh Mailemo ne ya bayyana hakan, inda ya ce irin kyakkyawan tunanin Kwankwaso da ya yi duba da tsakani ma’aikata da gwamnatin siyasa ba kowane lokaci ne akan samu buri ko buƙatar na dirar da ayyuka da gwamna ya ya zo da su a ɗan tsakanin lokuta da aka zaɓe shi akai ga gaci ba.

Ya yi nuni da cewa “domin ƙila in kazo da sabbin abubuwa ka samu tsaiko wajen aiwatarwa, saboda fahimtar ma’aikata ko idan ya kasance suna da wata alaƙa da wani tsari na daban, wannan ce ta sa tun a wancan lokaci a ƙoƙarin Kwankwaso na tabbatar da ƙudure-ƙudurensa sun kai ga gaci a tsakanin shekarun da zai yi akan gwamna ya ƙirƙiri dirkoki kusan biyar.”

Ya ce na farko akwai CRC da Lafiya Jari da Kwankwasiyya da Kano Proper da ita kanta jam’iyya wanda Kwankwasiyya da jam’iyya suna kula da abinda ya shafi harkar aƙida da jam’iyya tafiya ta siyasa ita kuma CRC tsari ne na yunƙurin jagora don ganin al’umma sun shiga cikin al’amuran gwamnati na tabbatar da tsarukan da aka zo da su sun samu amsuwa ga jama’a. Sannan ta samu damar gabatar da tsarurrukan ta da take so su dira har ƙasa cikin sauri.

Alhaji Habib Saleh Mailemo ya ce ɗaya daga cikin ƙudurin tsarin Kwankwasiyya shine inganta ilimi ta farfaɗo da shi don samar da al’umma da take da ilimi da za ta iya amfani da shi wajen kawo cigaba a kowane sassa na rayuwa. Idan kuma aka duba ma’aikatar ilimi tana da tsare-tsare na bai ɗaya da kusan duk ƙasa ita ake bi sai aka ɓullo da wannan don tallafawa ga inda wancan ya gaza.

Ya ce an samar da tsare-tsare da aka aiwatar da su ƙarƙashin CRC da suka taimaka wajen samun nasarar ta haɓakar ilimi a jihar Kano aka samu kyakkyawan sakamako na cigaban ilimi a lokacin Gwamnatin Kwankwaso wanda a yanzu ma ƙarƙashin Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ake aiwatar da su cikin nasara.

Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin lafiya jari an yi abubuwa da yawa na inganta harkar lafiya a jihar Kano har aka riƙa koyawa matasa sanin harkar magani da fito da tsarin duba marasa lafiya na tafi da gidanka ake zuwa karkara ana duba lafiyar al’umma duk irin waɗannan abubuwa an faɗaɗa su.

Ya ce babu wani jami’in gwamnati da za a laru da shi da za a ce shi zai sa ido kai tsaye ya ga an yi irin waɗannan abubuwa shi ne sai aka ƙirƙiri Kano Proper domin ta bibiyi irin waɗannan abubuwa da ake da tabbatar da cewa suna kaiwa ga ƙasa inda ake buƙata.

Ya ce in an ce a bada kayan sawa a makaranta da duk wani abu a tabbatar an kai an raba, sun kai ga inda ake buƙata da sa ido akan duk ƙudurin da gwamnati take aiwatarwa shine babban aikin Proper.

Alhaji Habibu Mailemo ya ƙara jaddada cewa babban aikin Proper shine tabbatar da an aiwatar da ƙudure-ƙuduren gwamnati sun kai ga gaci yadda ake buƙta. Bibiya da saka idanu da tabbatar da cewa dukkan ƙudiri na gwamnati da wani tsari da wani aiki da gwamnatin Kano ta ɗauko a kowane ɓangare a tabbatar aikin nan an yi shi.

Alhaji Habibu Saleh Muhammad Mailemo ya ƙara da cewa Proper tana aiki ne domin ta zaburar da al’umma su gane amanar da aka bai wa gwamna ta zaɓen da aka yi ya ɗora nauyin akan wasu da za su taimaka masa a tabbatar an riƙe wannan amanar.

By ukarofi