Daga USMAN KAROFI
Majalisar Dattawa ta nuna matukar damuwa kan wasu matsaloli da suka shafi rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, ciki har da rashin daidaito a kuɗi da kuma ɓacewar makamai.
Rahoton babban akanta janar na ƙasa ya bayyana cewa an samu rikice-rikicen kwangila da suka kai naira biliyan 1.136, tare da ɓacewar bindigogi sama da 3,900, ciki har da manyan bindigogin AK-47, waɗanda ake zargin sun faɗa hannun miyagu.
Ko da yake mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda mai kula da kasafin kuɗi, Abdul Suleiman, ya tabbatar wa da ‘yan majalisa cewa rundunar ta mayar da martani kan binciken, ‘yan majalisar sun buƙaci ƙarin bayani. Yayin zaman, wata jayayya ta ɓarke tsakanin ‘yan majalisar, inda Sanata Ningi ya buƙaci tattaunawa a sirrance sannan ya fice daga taron. Sai dai mafi yawan ‘yan majalisar sun dage cewa ya zama dole a bayyana wa jama’a abin da ke faruwa.
Sanata Victor Umeh ya soki ‘yan sanda da kasa gano makaman da suka ɓace, yana mai cewa rashin waɗannan bindigogi a irin wannan lokaci na matsananciyar rashin tsaro yana da matuƙar haɗari. Majalisar ta buƙaci Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya bayyana a gabanta a ranar Litinin domin bayar da ƙarin bayani kan lamarin.
