Daga UMAR GARBA a Katsina
’Yan kasuwa 10 daga Zariya ta jihar Kaduna sun rasa rayukansu bayan da motarsu ta afka kan wata babbar gada, hatsarin ya faru bayan da wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindinga ne suka buɗe wa motar wuta a hanyarsu ta zuwa Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan kasuwar kan yi tattaki daga kasuwar ɗanmagaji da ke Zariya, zuwa jihohin Katsina da Zamfara domin sarin tumatur, sai dai a wannan karon ‘yan kasuwar sun haɗu da iftila’in harin ‘yan bindinga a ƙauyen Takoki da ke ƙaramar hukumar Funtuwa ta Jihar Katsina a kan hanyarsu ta dawowa.
Mazauna yankin sun bayyana cewa direban motar ya yi yunƙurin juya wa da motar don komawa baya, bayan da ɓarayin dajin suka tsayar da shi, a ƙoƙarin tsere wa motar da ke ɗauke da ‘yan kasuwan ta ƙwace masa, inda ta faɗa kan wata babbar gada.
Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a yayin da wasu 7 suka samu raunuka.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Manhaja cewa, ɓarayin sun yi awon gaba da aƙalla ‘yan kasuwa biyar zuwa cikin daji, a yayin da aka ƙiyasta ‘yan kasuwar sun yi hasarar kayayyakin da suka sawo na kimanin Naira miliyan 60.
A halin yanzu, Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya bayyana alhininsa kan rasuwar ‘yan kasuwar.
Kakakin majalisar, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Musa Abdullahi Krishi, ya yi Allah wadai da harin baki ɗaya.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi don ganin an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su tare da kamo ‘yan fashin dajin.
Daga ƙarshe kakakin majalisar ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan kasuwar yare da yin addu’ar Allah ya jiƙan su da rahma.
