Mu na so a soke shirin maida makarantarmu Gusau – Ƙungiyar Matasan Zurmi

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙungiyar tuntuɓa da cigaban matasan Zurmi a Jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnan Zamfara Dauda Lawal da ya janye shirin mayar da makarantar koyon aikin jinya da ungowar zoma ta Zurmi Gusau saboda rashin tsaro.

Mataimakin shugaban ƙungiyar Kwamared Abba Modibbo ne ya yi wannan kiran a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja a Gusau yau litinin.

A cewar sa kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da yadda ƙaramar hukumar Zurmi tana a shiyyar majalisar dattawa ta Zamfara ta Arewa wadda aka bar ta a baya wajen ayyukan raya ƙasa da ka iya yin tasiri kai tsaye ga al’ummar yankin.

Ya Ƙara da cewa, shirin da ake zargin yana yaɗuwa a kafafen sada zumunta na zamani cewa gwamnatin jihar ta kammala duk wani shiri na mayar da makarantar zuwa Gusau babban birnin jihar sakamakon rashin tsaro da ya addabi yankin wani babban ƙalubale ne a rayuwar mutanen yankin.

“Batun rashin tsaro ba yankin mu bane kaɗai ya shafa, kuma wannan makaranta da muka daɗe ana jira da gwamnatin jihar ake zargin tana shirin mayar da ita zuwa wani yanki na jihar sam bai dace ba”. Ya ƙara da cewa

A cewar sa, ya kamata hukumomi su ɗauki ƙwararan matakan shawo kan lamarin tsaro maimakon mayar da makarantar Wani wuri na daban.

Ya ce, alummar garin Zurmi a Zamfara suna fuskantar ƙarancin abubuwan more rayuwa kamar hanyoyin sadarwa, wutar lantarki da samar da ruwan sha wanda sun shafe shekaru da dama a wannan yanayin.

Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta duba manyan ƙalubalen da suke fuskanta domin ci gaban yankin ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.

“Sama da shekaru bakwai muna cikin rashin wutar lantarki kuma a shekarar da ta gabata mun fuskanci ƙalubale na lalata layin mu na sadarwa (MTN Mast Antenna) da ‘yan ta’adda suka yi, kuma mun kwashe sama da shekaru goma ba tare da ruwan sha ba, don haka muka buƙaci gwamnatin jihar da ta gaggauta duba wannan lamarin domin ci gaban mu. Ya bayyana

Kwamared Abba Modibbo ya yi nuni da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da zama ‘yan ƙasa masu bin doka da oda tare da marawa gwamnati baya domin ci gaban jihar.

Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha na Jihar Alhaji Wadatu Madawaki kan lamarin da wakilinmu ya yi ya ci tura domin har zuwa lokacin haɗa rahoton bai samu magana dashi ta wayar Salula ba.

By ukarofi