
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kula da ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) a Legas, ta gano wajen da aka ɓoye wasu magungunan bogi da suka haɗa da na ƙanjamau (HIV) da kodin na ruwa, a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan raba magungunan bogi a cikin al’umma.
Lamarin ya biyo bayan rufe shaguna 3,000 ne na Idumota da hukumar ta yi a jihar sakamakon yaɗa magungunan bogi da baragurbin mutane ki yi wa jama’a.
A wata takarda da ta fitar a ranar Litinin, NAFDAC ta ce ta kuma gano wasu ɗakuna biyu na ajiyar magungunan bogi da waɗanda wa’adinsu ya cika a garin Aba da kuma wasu tireloli a Idumota da Onitsha.
Sanarwar ta ce daga cikin abubuwan da aka gano akwai na riga-kafi da aka ajiye su a wajen da babu wadatacciyar iska, da tarin alluran Analgin, wadda an haramta amfani da ita da na HIV waɗanda wa’adinsu ya cika da kuma waɗanda ba a yi masu rajista ba da dai sauransu.
Haka kuma, ta ce ta kama haramtattun magunguna da adadinsu ya kai tirela 12, waɗanda suka haɗa da holoƙon kwalaye na allurar zazzaɓin cizon sauro da ba a yi wa rajista ba kuma wa’adinsu ya ƙare.
Bugu da ƙari, ta kama tarin kodin da Tiramol 225 a wata kasuwa da wasu nau’ukan haramtattun harkokin magunguna a wurare daban-daban.
