Gwamnonin Arewa maso Yamma su ajiye bambancin siyasa gefe domin cigaban yankin – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar hukumar cigaban yankin Arewa maso Yamma

Gwamnan ya jinjina wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da majalisar tarayya bisa ƙirƙirar hukumar wanda yace zata ciyar da yankin gaba.

Ya bayyana matsalar tsaro a matsayin babban damuwar yankin,amma ya ce jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarin su wajan shawo kan matsalar,”kuma muna cigaba da ɓullo da duk wata hanya da zasu kawo ƙarshen matsalar”inji Dikko.

Haka kuma gwamnan ya bayyana bunƙasa noma da ilmi zai kawo gagarumin bunƙasa tattalin arzikin yankin,ganin noma shine ƙashin bayan tattalin arzikin yankin.

Ya cigaba da cewa a ƙoƙarin gwamnatin sa na bunƙasa ilimi a jihar, gwamnatin sa ta ɗauki malaman makarantun aikin dindindin har guda 7,325 tare da gina manyan makarantun sakandare guda 150.

Malam Dikko Raɗɗa yaba hukumar tabbacin cewa gwamnonin Arewa zasu bada cikakken goyon baya.

Tunda farko sanatan shiyar Funtua Sanata Muntari Ɗandutse,kuma mataimakin kula da hukumar Arewa maso Yamma a majalisar dattijai ya shaidawa gwamnan cewa sun kawo ziyarar ban girma ne da kuma neman shawarwarin sa ta yadda za a ciyar da yankin gaba.

Shi kuwa a nasa jawabin shugaban hukumar Farfesa Shehu Abdullahi ma’aji ya bayyana wa gwamnan cewa wannan hukuma ba kishiyar gwamnonin Arewa maso yamma ba ne yace sai da takwarar su ce wajan cigaban yankin.

Ya ce wannan hukuma za ta samar da ayyukan raya ƙasa domin farfaɗo da yankin wanda ya sami naƙasa sanadiyyar matsalar tsaro.

By ukarofi