Gwamna Raɗɗa ya sanya sunan ƙasar Qatar a shatale-talen gidan gwamnati

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Domin kyautata alaƙa tsakanin Jihar Katsina da gwamnatin Ƙasar Qatar, Gwamna Raɗɗa ya saka sunan ƙasar a titin Shatale-talen gidan gwamnati

A ranar Talata 18 Fabrairun 2025, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD,CON, ya karɓi baƙuncin jakadan ƙasar Qatar a Najeriya Dakta Ali Ghanem Al-Hajri, a wata ziyarar kyautata alaƙa tsakanin ƙasar da Jihar Katsina.

A lokacin ziyarar, gwamnan Raɗɗa ya nuna mashi irin al’adun ƙasar hausa da suka haɗa da raye-rayen gargajiya, shigar sarauta da hawan dawaki, dambe, da sauran su.

Bayan kammala wasannin gargajiyar, gwamnan ya bayyana titin da ya tashi daga shatale-talen gidan gwamnati ya isa hanyar zuwa Ƙofar Sauri, a jikin shagon A.K da sabon sunan da aka bashi na “Qatar Street” ma’ana titin Qatar.

Wanda suka halarci wajen akwai mataimakin gwamnan Hon. Faruk Lawal Jobe, Kwamishinan ayyuka Injiya Sani Magaji, da sauran Su.

By ukarofi