Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu, ya miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna mutane 59 da jami’an tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.
Waɗanda aka ceto ɗin sun haɗa da manya maza 28, manya mata 24 da yara shida, waɗanda aka ceto su daga wurare daban-daban a jihar Kaduna.
A jawabinsa, Ribadu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a aikin haɗin gwiwa da ɗaukacin jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Bola Tinubu su ka yi na ƙara ƙaimi wajen ganin an samu zaman lafiya da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan.
“A yau, mun karɓi waɗanda aka kuɓutar daga hannun ‘yan fashin daji da su ka yi garkuwa da su.
“Za mu maida kowa gidan su mun riga mun gana da su. Haka lamarin ya ke kasance wa,” inji Ribadu.
