Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar PDP ta bai wa ‘yan majalisar wakilai da majalisar dokokin umarnin barin kujerunsu tun da sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
‘Yan majalisa yankin Kaduna ta Kudu na daga cikin mutane 50 da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Gwamnna jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ne ya karɓi waɗanda suka sauya sheƙar ciki har da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero da tsohon sanata Danjuma La’ah a yayin wani gangamin taro da aka yi a babban filin taro na Murtala Sƙuare a Kaduna.
Jam’iyyar PDP dai ta yi Alla-wadai da wannan mataki kamar yadda Maria Dogo mai sakatariyar jam’iyyar ta bayyana a ranar Lahadi a Kaduna. Ta ce sauyin sheƙar, musamman daga ‘yan majalisu masu ci a yanzu babbar cin amana ce ga mutanen da suka yi amanna da su.
Mrs Dogo ta ce PDP na maraba da ‘yancin damar shiga kowacce ƙungiya, amma ba ta maraba da wannan sauyin sheƙa da tsofaffin ‘ya’yanta suka yi.
“Don haka, muna tabbatar wa da al’ummar jihar Kaduna, musamman waɗanda wannan sauyin sheƙa ya shafa cewa za mu shugabancin jam’iyyar zai yi amfani da kundin tsarin mulki domin ƙwato waɗannan kujeru domin kan jam’iyyar a haɗe yake har zuwa mataki na ƙasa.”
“Sashen na na 68(1)(g) da na 109 na kundin tsarin mulki ya tanadi cewa idan ɗan majalisa mai ci ya sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya dole ne ya sauka daga kan kujerarsa.”
“Muna kira ga kakakin majalisar wakilai da na majalisar dokokin jiha da su ayyana kujerunsu a matsayin babu kowa a kansu da kuma sanar da hukumar zaɓe mai zaman kanta domin ta gudanar da zaɓen cike gurbi.”
“PDP za ta cigaba da tsayawa ƙyam domin ita ce zaɓin al’ummar jihar Kaduna.”
“A fili yake cewajam’iyyarmu ta mutane ce idan aka yi la’akari da zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a kwanakin baya wanda mutane suka kafa, suka tsare daga ƙin ba wa APC damar ƙaƙaba musu ‘yan takararta duk da ba kunya ba tsoron Allah haka aka ayyana ‘yan jam’iyyar a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen.”
Ta ce akwai waɗanda sakamakon rasa cikar muradinsu ya sa suka riƙa yi wa APC aiki ta ƙarƙashin ƙasa kuma sauyin sheƙar da suka yi, sun yi ne domin samun tikiti a shekarar 2026 saboda APC jam’iyya ce da ba ta zaɓen cikin gida.
“Muna ƙalubalantar gwamnan da ya sake fasalin muƙararrabansa kuma ya bai wa waɗanda suka sauya sheƙar muƙamai idan da gaske yake ya yarda da nagartarsu.”
“Sannan muna kiran gwamnatin Kaduna da ta daina almubazzaranci da kuɗin harajin jihar Kaduna wajen shirya tangamamen taro na karɓar sabbin ‘yan jam’iyya.”
A maimakon haka, ta shawarci gwamnatin da ta mai da hankali wajen raba wa al’umma romon dimokraɗiyya wanda mutane ke ta kishi tun bayan hawansa mulki.
“Gaskiyar magana ita ce mutane ba su da burin da ya wuce ganin jam’iyyar PDP ta dawo mulki a jihar Kaduna saboda irin yadda a baya al’umma suka samu cigaban tattalin arziƙi da iya biya wa kansu buƙatu na yau da kullum.”
Don haka ta ce, ko ma sau nawa za a sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ba zai hana gwamnatin yin sallama da gidan gwamnati ba a shekarar 2027.
Mrs Dogo ta ƙara da cewa shugabancin Edward Masha, shugaban jam’iyyar PDP a jihar, zai cigaba da mayar da hankali ga kare dimokraɗiyya da tabbatar da muradan al’umma.
