Kan APC a haɗe yake a jihar Katsina – Maituraka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Jigo a Jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Abdulaziz Maituraka ya ce kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Katsina a haɗe yake kuma suna aiki tare a matsayin ‘yan uwa.

Maituraka ya yi wannan magana ne a hira da ya yi da manema labarai a Katsina kan zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a jihar.

Ya bayyana nasarar da jam’iyyar ta samu a zaɓen da ya gudana wanda hakan ya nuna ƙarfin da jam’iyyar ke da shi a jihar, “saboda haka mun shirya tunkarar zaɓen 2027,” inji shi.

Maituraka ya ƙara da cewa nasarar zaɓen ya kuma nuna irin goyon baya da masu ruwa da tsaki cikin su har da tsohon gwamnan jihar Aminu Bello Masari ke badawa ga gwamnatin Dikko Raɗɗa da APC a jihar.

Sai ya yi kira ga zaɓaɓɓen shugabanni da kansilolin da su tashi tsaye wajen inganta rayuwar mata da matasa da aiwatar da ayyukan raya ƙasa a yankunansu.

Jigo a jam’iyyar APC ya kuma yi kira ga jama’a da ‘yan soshiyal midiya da su guji yaɗa labaran ƙarya dangane da abinda ya shafi harkar tsaro.

A cewarsa, gwamnatin Dikko Raɗɗa na iyaka ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar, “ya kamata jama’a su bada tasu gudummawa na taimaka wa gwamnatin wajen tabbatar da tsaro a jihar.”

Ya bayyana zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a matsayin zaɓe mai sahihanci, Maituraka sai ya yaba wa masu zaɓe da suka fita da yawansu zuka zaɓi waɗanda suke so.

By ukarofi