Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin gudanar da bincike a kan zargin karkatar da kayayyakin agajin da aka bai wa ’yan gudun hijira a Abuja.
Kwamishinan Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira na Tarayya, Aliyu Ahmed ne ya bayyana haka bayan gano kayan agajin da aka ɓoye a ajujuwa a sansanin ‘yan gudun hijira na Durumi da ke Abuja.
Ahmed wanda ya je sansanin ‘yan gudun hijira na Durumi ne domin ƙaddamar da wata cibiyar na’ura mai kwakwalwa da gidauniyar Brand Life ɓision Foundation ta bayar, ya fara duba sansanin inda ya gano cewa ajujuwa ne ake ajiye kayan abinci da na abinci da za a rabawa ‘yan gudun hijirar, amma aka ƙi.
“A lokacin da muka isa, mun ga abubuwa da yawa da bai kamata a yi hakan ba a sansanin. Mun ga halin da ake ciki inda aka yi amfani da wasu ajujuwa wajen adana kayan abincin da ya kamata a raba wa ‘yan gudun hijira. Ba za ji daɗin hakan ba. Za mu shawo kan lamarin,” inji shi.
Kwamishinan ya bayyana shirin kafa wani kwamiti da zai binciki irin wannan lamari a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ke faɗin ƙasar nan.
“Abin da muka gani a nan yana da ban tsoro. Za mu faɗaɗa bincikenmu zuwa wasu sansanonin saboda idan abin yana faruwa a nan, yana iya faruwa a wani wuri,” inji shi.
Hukumar ta bai wa ‘yan gudun hijira tabbacin ci gaba da jajircewar gwamnati wajen kyautata rayuwarsu.
Ta kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa ilimin ‘yan gudun hijira ta hanyar yin aiki tare da Hukumar Ilimi ta Bai ɗaya don samar da malamai ga yaran da suka rasa matsugunansu.
A nata jawabin, shugabar gidauniyar Brightlife ɓision, Hajia Binta Sidi, ta bayyana shirin horar da ‘yan gudun hijira 1000 a faɗin kƙsar nan.
A cewarta, gidauniyar ta shafi yara marasa galihu, ‘yan gudun hijira, da marayu.
Yayin da ta yaba wa hukumar kan samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga Cibiyar horarwa ta ICT, ta bayyana cewa gidauniyar za ta samar da malaman da za su riƙa horar da ‘yan gudun hijirar.
