Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A cikin shekara biyu, gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki mutane 34,000 aiki a fanni daban-daban a faɗin jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a wajen bikin bada tallafin kuɗi ga mata 600 domin inganta kiwo ƙarƙashin Gidauniyar Kabir Magaji Gafiya a garin kaita.
Gwamnan wanda ya sami wakilci na mataimakin gwamnan jihar malam Farouk Lawal Joɓe ya ce babu wata gwamnati a ƙasan nan da ta ɗauki adadin waɗannan mutane aiki.
Hakan ya nuna ƙoƙarin gwamnatin Dikko Raɗɗa na rage aikin yi da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar a cewar mataimakin gwamnan.
Ya bayyana cikin waɗanda aka ɗauka aiki akwai ta fanin addini inda ake bawa Limamai da ladanai na masallacin juma’a alawus ko wane wata.
Joɓe ya ce lokacin da suka hau mulki Jihar Katsina nada ma’aikata 22000 da SUBEB suna da ma’aikata 25000.
Ya kuma bayyana mahimmancin zuba jari akan harkar noma da kiwo wanda akan haka gwamnatin jihar ta ba mata da masu kiwo su 40000 tallafi na Naira biliyan 5.7.
Tallafin ya haɗa da Awaki na kiwo da abincin su da magungunan su da malaman kiwon lafiya da zasu kula da dasu da sauran su.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa manufar gwamnati na wannan shiri a nan gaba gwamnati ta rinƙa fitar da awakan zuwa ƙasar Saudi Arabia da sauran wasu ƙasashen duniya.
A jawabin sa Dr Kabir Magaji Gafiya wanda shine shugaban SUBEB a jihar ya bayyana wannan tallafin kuɗi a matsayin mai da biki ga ya’yan jam’iyyar APC a jihar.
