
Daga BELLO A. BABAJI
Ana hasashen bashin Nijeriya a Bankin Duniya ka iya ƙaruwa da Dala biliyan 9.2 matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya ciyo bashi guda shida da adadinsu ya kai Dala biliyan 2.23 a shekarar 2025 da ya ke shirin yi.
Hakan na nuna yadda ƙasar ke cigaba da dogaro da bashi don tallafa wa manyan ɓangarori harkar tattali waɗanda suka haɗa da lafiya da ilimi da sauran su.
A shekarar 2023 ne Bankin Duniya ya amince da bai wa Nijeriya bashin da Dala biliyan 2.7 don gudanar da ayyukan samar da makamashi, ilimi da lantarki.
Daga cikin shirye-shiryen da aka gudanar da su akwai inganta mata da harkokin samar da makamashi da shirin tallafa wa ɗalibai mata da sauransu.
Bashin na ƙaruwa ne sakamakon tallafin kuɗi da harkar tattalin Nijeriya ke buƙata don yalwata wa ɓangaren.
Ga shekarar 2025, Nijeriya na neman ciyo bashi ne don ɓangarori guda shida da suka haɗa da na ababen more rayuwa, na harkokin dijital, lafiya da ilimi da abinci da kuma inganta wasu ababen more rayuwa a sassan ƙasa.
