Daga USMAN KAROFI
Hukumar kula da Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta amince da ƙarin bankuna uku domin tallafawa aiwatar da shirin adashen kuɗi na hajji. Waɗannan bankuna sun hada da Taj Bank, Alternative Bank da Lotus Bank, waɗanda za su yi aiki tare da Ja’iz Bank, wanda ke cikin shirin tun farko.
A cewar Abdulbasit Abba, jami’i a sashen bayanai da wallafa na NAHCON, an gudanar da bikin rattaɓa hannu da karɓar takardun amincewa a hedikwatar NAHCON da ke Abuja. Wakilan bankunan uku sun karɓi takardunsu daga hannun kwamishinan tsare-tsare, ma’aikata, Kula da Kuɗaɗe, Prince Abdullazak Aliu, a madadin Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman.
NAHCON ta bayyana cewa wannan ci gaba zai ƙara ƙarfafa tsarin hada-hadar Kuɗaɗe don shirye-shiryen aikin hajji ga al’ummar Musulmin Najeriya. Wannan shiri zai ba maniyyata damar ajiya da tanadin kuɗinsu cikin sauƙi da tsari mai inganci.
