Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin da za ta riƙa sa ido akan kaucewa afkuwar gobara da ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.
Za a kafa wannan kwamiti ne a kowace ƙaramar hukuma ƙarƙashin kulawan hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA).
Da yake ƙaddamar da kwamitin , mataimakin gwamnan jihar malam Farouk lawal Joɓe wanda ya wakilci gwamnan jihar malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa aikin kwamitin shine fito da tsare tsare ta yadda za a magance matsalolin samun wannan iftala’i a jihar.
Ya sanar da cewa gwamnati ta kafa kwamitin a kowace ƙaramar hukuma,sannan su kuma za su kafa irin wannan kwamiti a matakin gundumar domin kawo ƙarshen wannan bala’i da ke jawo asarar rayuka da dukiyar al’umma.
Joɓe ya bayyana cewa kwamitin za su yi aiki kafaɗa kafaɗa da hukumar SEMA ta jihar domin samun nasarar wannan yunƙuri na gwamnatin Dikko Raɗɗa.
Sai yayi kira ga ƙananan hukumomi da su ba kwamitin haɗin kai da ya kamata domin samun nasarar wannan gagarumin aiki da aka basu .
Shugaban hukumar SEMA a jihar Hajiya Binta Hussaini Dangani ta bayyana dalilan kafa wannan kwamiti a ƙananan hukumomi da tace gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin kaucewa irin ɓarna da ruwan sama a bara ya haifar a jihar.
Haka ne yasa hukumar ta kafa wannan kwamitoci a yankunan karkara da cikin birane a jihar domin shawo kan irin wannan iftala’i da kuma tsara yadda za a riƙa taimakawa al’umma da zarar hakan ya faru a cewar ta.
Kwamitin ya haɗa da hukumar kashe gobara da jami’an tsaro,da shugabannin al’umma.
