Matar Akpabio ta ƙaryata zargin cin zarafin Natasha da alwashin zuwa kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Matar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Misis Ekaetta Unoma Akpabio, ta yi watsi da zargin cin zarafi da Sanata Natasha ta yi wa mijinta a wata hira ta gidan telebijin.

A yayin ganawa da manema labarai, matar shugaban majalisar ta bayyana kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin iyalanta da na Natasha inda ta yi watsi da kalaman sanatar da cewa ba haka suke ba.

Ta hasato batun ranar 8 ga watan Disambar 2023 da Natasha da mijinta suka kai wa Akpabio ziyara a gidansa, inda ta ce ta nan a lokacin da suka je gidan.

Ta ce, iyalan biyu sun jima suna sada zumunci a tsakanin su tun kafin Natasha ta auri mijinta.

Misis Akpabio ta kuma yabi mijin nata da cewa mutum ne da ya samu gogewa a rayuwa, wanda ke son iyalansa da mutunta su, ta na mai bada shaidar sa da goyon baya da taimaka wa tsarin damawa da mata a harkokin gwamnati tun kafin ya zama shugaban majalisar.

Matar shugaban majalisar ta kuma yi kira ga mata da su ƙaurace wa kururuta zargi na ƙarairayi da kuma alwashin ɗaukar matakin doka.

By Babaji