Daga ABUBAKAR A BOLARI
Babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba ta 7 ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Fatima Musa ta ɗage sauraron shari’ar rikicin fili tsakanin kamfanin Emir General Integrated Limited da kamfanin gine-gine na Grand Scope Construction Limited zuwa ranar 20 ga watan Maris, 2025.
Hakan ya biyo bayan buƙatar gwamnatin Jihar Gombe ta shiga cikin shari’ar domin bayyana matsayinta kan rikicin.
Lauyan mai gabatar da ƙara, Suleiman Abdurrahim, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta nemi shiga cikin shari’ar ne domin tabbatar da adalci a kan rikicin filin da ake taƙaddama a kansa.
“Shigowar gwamnati zai taimaka wajen ganin an cimma adalci,” in ji lauyan, wanda ya ƙara da cewa, tun farko gwamnati ba ta cikin ɓangarorin da ake ƙara, sai dai kamfanin gine-gine na Grand Scope Construction Limited.
Rikicin ya samo asali ne daga wani fili da kamfanin Emir General Integrated Limited ya mallaka a kan hanyar Gombe zuwa Bajoga. Gwamnatin jihar ta fara amfani da filin wajen gina garejin zamani da ake kira Mechanic Village, inda aka bai wa kamfanin Grand Scope Construction Limited kwangilar gudanar da aikin gine-ginen.
Mai filin, Emir General Integrated Limited, ya kai ƙara gaban kotu yana zargin kamfanin Grand Scope da shiga filinsa ba tare da izini ba, lamarin da ya haddasa wannan rikici.
A zaman da aka yi ranar Litinin, Lauyan mai ƙara ya bayyana cewa kamfanin Grand Scope Construction Limited ya karya umurnin kotu na dakatar da su daga cigaba da aikin gine-ginen a filin.
“Kamfanin ya ƙi bin umarnin da kotu ta bayar. Wannan ya nuna rashin girmamawa ga doka,” in ji Lauyan, wanda ya buƙaci kotun ta ɗauki matakin kama daraktocin kamfanin saboda karya dokar kotu.
Lauyan ya ƙara da cewa babu wata matsala kan shigar gwamnati cikin ƙarar, yana mai cewa, “Shigowar gwamnati zai bayyana gaskiya tare da kawo ƙarshen rikicin.”
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin kamfanin Grand Scope Construction Limited, amma lauyan su bai tsaya ba bayan fitowa daga kotun.
Bayan sauraron ɓangarorin da suka gabatar da buƙatunsu, kotun ta ɗage cigaba da shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Maris, 2025, domin sauraron buƙatar gwamnatin jihar tare da yanke hukunci kan abin da ya dace game da shigar da gwamnatin cikin ƙarar da kuma zargin karya dokar kotu da ake yi wa Grand Scope Construction Limited.
