
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na Hukumar kula da Ɗalibai Masu yi wa ƙasa Hidima, wato NYSC.
Kafin naɗinsa, Birgediya Kunle shi ne shugaban ma’aikatan Shugaban Sojojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede.
Sabon shugaban hukumar, mamba ne na ƴan zangon karatu na 47 na sojojin Nijeriya, kuma jami’in ‘Artillery’ ne da yayi karatu a Kwalejin Sojoji da Kwalejin Koyon Yaƙi dake Amurka.
Haka kuma, ya riƙe muƙamin Daraktan Ma’aikata a Kwalejin Koyon Yaƙi ta Nijeriya.
Birgediya Janar Kunle ɗan asalin garin Ileogbo ne dake Ƙaramar Hukumar Aiyedire a Jihar Osun.
Sabon muƙamin da ya samu na nufin cewa ya maye gurbin Birgediya Janar Yusha’u Ahmed.
