
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta-janar na Ƙasa (AGF) biyo bayan tantancewa mai fadi da aka gudanar akansa.
Naɗin Ogunjimi, wanda aka tabbatar a ranar 4 ga watan Maris, zai fara aiki ne a ranar 7 ga watan Maris, 2025, kuma a ranar ne mai barin gado, Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya.
A watan Disambar da ta gabata ne aka ayyana Ogunjimi mai shekaru 57, a matsayin wanda zai gaji Madehin a muƙamin.
An naɗa shi ne bayan cin jarrabawar da wani kwamiti ya yi masa gami da tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki, wanda ke nuna ƙoƙarin Shugaba Tinubu na tabbatar da adalci a yayin naɗa wani muƙami.
Ogunjimi ya kammala digirinsa na farko ne a Jami’ar Nsukka, a shekarar 1990, a tsangayar nazarin Akantanci. Haka kuma ya yi na biyu a irin tsangayar, a Jami’ar Legas.
Kazalika, mamba ne shi a Cibiyar Kwararrun Akantawa ta Ƙasa da kuma ta Cibiyar Nazarin Haraji ta Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya taya shi murna tare da kira a gare shi da ya gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da adalci da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima.
