Ahmed Musa ya shiga sahun ƴan Super Eagles da za su fafata a wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kocin Super Eagles, Éric Sékou Chelle ya zaɓi masu tsaron gida Stanley Nwabali da Adeleye Adebayo, da ƴan wasan baya William Ekong, Calvin Bassey da kuma Olaoluwa Aina

Sai ƴan wasan tsakiya Alex Iwobi da Wilfred Ndidi, da kuma na ƴan wasan gaba Ademola Lookman, Victor Osimhen and Simon Moses daga cikin jaddawalin ƴan wasa 39 da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026 da ƙasashen Rwanda and Zimbabwe da za a yi a wannan watan.

Haka kuma, akwai gola Maduka Okoye da ƴan baya da suka haɗa da Bruno Onyemaechi da Zaidu Sanusi, sai na tsakiya Frank Onyeka da Fisayo Dele-Bashiru, da kuma ƴan gaba irin su Ahmed Musa, Samuel Chukwueze da Sadiq Umar.

Kamar yadda Blueprint ta ruwaito, akwai ƴan wasa kamar su Igoh Ogbu, Ifeanyi Onyebuchi, Anthony Dennis, Chrisantus Uche, Papa Daniel Mustapha, Tolu Arokodare da kuma Jerome Akor Adams waɗanda wannan shi ne karo na farko da aka kira su.

Sai kuma ƴan wasan da ke taka wa a gida Nijeriya da suka haɗa da mai tsaron gida Kayode Bankole, ɗan baya Jordan Torunarigha, ɗan tsakiya Joseph Ayodele-Aribo da ƴan gaba Cyriel Dessers da kuma Nathan Tella, matuƙar suka shiga sahun guda 23 da za a yi wa tantancewa ta ƙarshe.

Nijeriya ita ce ta biyar a rukunin C, wato ƙasa da Rwanda, Afirka ta Kudu, Jamhuriyar Benin da Lesotho, inda Super Eagles za ta fafata da Rwanda a Kigali a ranar Juma’a, 21 ga watan Maris, kafin daga bisani ta buga da Zimbabwe Warriors a filin Godswill Akpabio Stadium a Uyo dake Jihar Akwa-Ibom bayan kwanaki huɗu.

Ga jaddawalin ƴan wasan Nijeriya 39 da ake sa ran za su fafata da ƙasashen biyu, kamar yadda Blueprint ta ruwaito:

“Goalkeepers: Stanley Nwabali (Chippa United, South Africa); Maduka Okoye (Udinese FC, Italy); Amas Obasogie (Singida Blackstars, Tanzania); Adeleye Adebayo (Enosis Paralimni, Cyprus); Kayode Bankole (Remo Stars)”

“Defenders: William Ekong (Al-Kholood FC, Saudi Arabia); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce SK, Turkey); Bruno Onyemaechi (Olympiacos FC, Greece); Gabriel Osho (AJ Auxerre, France); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Igoh Ogbu (SK Slavia Prague, Czech Republic); Jordan Torunarigha (Gent FC, Belgium); Ifeanyi Onyebuchi (Rangers International).”

“Midfielders: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Alhassan Yusuf Abdullahi (New England Revolution, USA); Fisayo Dele-Bashiru (Lazio FC, Italy); Frank Onyeka (Augsburg FC, Germany); Alex Iwobi (Fulham FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Anthony Dennis (Goztepe SK, Turkey); Chrisantus Uche (Getafe CF, Spain); Papa Daniel Mustapha (Niger Tornadoes).”

“Forwards: Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Victor Osimhen (Galatasaray FC, Turkey); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Kelechi Iheanacho (Middlesbrough FC, England); Victor Boniface (Bayer Leverkusen, Germany); Simon Moses (FC Nantes, France); Sadiq Umar (Valencia FC, Spain); Nathan Tella (Bayer Leverkusen, Germany); Cyriel Dessers (Glasgow Rangers, Scotland); Tolu Arokodare (KRC Genk, Belgium); Chidera Ejuke (Sevilla FC, Spain); Paul Onuachu (Southampton FC, England); Ahmed Musa (Kano Pillars); Jerome Akor Adams (Sevilla FC, Spain).”

By Babaji