‘Yan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Paradang

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, David Shikfu Parradang, ya rasa ransa a hannun wasu ƴan bindiga a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa sun bi sahunsa daga banki inda ya cire kuɗi, sannan aka yi garkuwa da shi a yankin Area 1 a safiyar Talata. Bayan an karɓe masa kuɗaɗen, miyagun sun kashe shi a take.

Wannan mummunan lamari ya sake jefa damuwa kan matsalar tsaro a babban birnin tarayya, musamman yawaitar sace mutane da kisan kai. Wani da ya tabbatar da faruwar lamarin ga News Point Nigeria ya bayyana alhinin sa, yana mai cewa, “Abin baƙin ciki ne jin cewa an kashe ɗan’uwanmu David Parradang. Allah ya jiƙansa.”

Jami’an tsaro sun fara bincike kan yadda aka yi garkuwa da shi da kuma kisan nasa, tare da ƙoƙarin kama waɗanda suka aikata wannan ta’addanci. Hukumar shige da fice ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, sai dai wani tsohon abokin aikinsa ya tabbatar da labarin. Har ila yau, ƙoƙarin jin ta bakin ‘yan sanda bai samu ba yayin da kakakin rundunar Abuja ba ta amsa kiran waya ko sakon tes ba.

By ukarofi