Majalisar Dattawa ta ce ba za ta binciki Akpabio kan zargin cin zarafin Natasha ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattawa ta ce ba za ta gudanar da bincike akan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ba, wanda aka zarge shi da cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, saboda ba a shigar mata da ƙara a rubuce ba.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti ta Kudu) ya bayyana hakan a yayin hira da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, inda ya ce wajibi ne kowane ɗaya daga cikin mambobin majalisar ya kula da irin kalaman da za su riƙa fitowa daga bakinsa.

Ya ce, a matsayinsu na cibiya, ba za su tanka akan abinda aka yi hirarsa a gidan telebijin ko ya fito daga wani nau’in fagen yaɗa labarai ba.

Adaramodu, ya kuma ce kasancewar su na ɗaya daga cikin rassan gwamnati, suna aiki ne a ƙarƙashin majalisar dattawa ko ta wakilai, ya na mai cewa ba sa aiki da abinda ke yawo a Soshiyal Mediya.

Ya bayyana cewa, lallai sai an miƙa masu jawabi a rubuce kafin su fara gudanar da bincike, ba kawai don yawo da batun ya ke yi a kafafen sadarwa suke la’akari da shi ba.

A lokacin da ya ke tsokaci game da batun wajen zama da ya fara haifar da rikicin, Adaramodu ya ce wajibi ne Sanata Natasha ta miƙa wuya ga dokokin gudanar da majalisar.

Dokar majalisar ta shar’anta wa ƴaƴanta yin magana da zama a kujerar da aka ware wa kowane ɗaya daga cikin su wanda rashin yin hakan saɓa wa doka ne.

Matuƙar sanata ya kiyaye ƙa’idar, babu shugaban majalisar da zai ƙi girmama shi, ko da kuwa shi shugaban ne da kansa, kamar yadda Adaramodu ya bayyana.

By Babaji