Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin rarraba kuɗaɗen asusun tarayya (FAAC), ya bayyana cewa har yanzu ba ta iya aiwatar da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na rabon kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye ba saboda akasarin su ba su bada asusun banki ba.
Ta ce ƙananan hukumomi 25 na jihar Delta ne kawai daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ke tarayyar Nijeriya suka cika sharuɗɗan rabon kuɗaɗen kai tsaye.
FAAC a makon da ya gabata ta gudanar da taronta, inda ta raba Naira tiriliyan 1.703 ga gwamnatin tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi a matsayin kuɗaɗen shiga na watan Janairun 2025.
Duk da haka, ta ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki na biyan hannun jarin jihohi da na ƙananan hukumomi cikin asusun haɗin gwiwarsu daban-daban.
A shekarar da ta gabata ne dai majalisar dokokin ƙasar ta amince da ƙudurin dokar cin gashin kan ƙananan hukumomi, wanda daga bisani shugaban ƙasar ya sanya wa hannu ya zama doka. Sai dai hakan bai yi wa gwamnonin jihohin daɗi ba, inda suka garzaya kotun ƙoli suna fatan bata dokar cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Sai dai a ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun ƙoli ta yanke hukuncin cewa ƙananan hukumomi, kasancewar su ne mataki na uku na gwamnati, su kasance masu cin gashin kansu tare da karɓar kason su kai tsaye daga FAAC.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ofishin Akanta Janar na tarayya Mista Bawa Mokwa ya shaida wa wakilinmu cewa kawo yanzu ba a san irin shirin da ƙananan hukumomin ke yi ba.
Ya bayyana cewa ya kamata su buɗe asusu a babban bankin Nijeriya ko kuma sun nuna cewa suna son a biya su ta ofishin biyan albashi na tarayya a jihohinsu, amma ba su yi hakan ba.
A cewarsa, “ƙananan hukumomin jihar Delta ne kawai suka kammala ayyukansu, amma ba za a iya biyan su kadai ba; har yanzu suna jiran wasu su shirya.”
Ya ce saboda rashin yanke hukunci na ƙananan hukumomin ne ya sa Akanta Janar na Tarayya ya gargadi jami’an gwamnatin tarayya na biyan albashi, a yayin rangadin da ta ke yi a ofisoshin biyan albashi na gwamnatin tarayya a kasar nan, da su tabbatar da cewa babu wata ƙaramar hukuma da za ta rika gudanar da asusu tare da bankin kasuwanci, inda ta dage da cewa su tabbatar da aiwatar da cikakken aiki da asusun ajiyar kudi na ‘Treasury Single Account (TSA)’ a dukkan ƙananan hukumomin.
Ana ta raɗe-raɗin cewa shugabannin ƙananan hukumomi na fargabar faɗawa cikin fushin gwamnonin jihohin idan har suka ci gaba da shirin samun rabon kuɗaɗen kai tsaye.
