Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Cibiyar fafutukar yaƙi da con hanci da rashawa a Nijeriya ta SERAP ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umurci Olayemi Cardoso, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya dakatar da aiwatar da ƙarin cajin hada-hadar kuɗi na katin ATM har sai an saurari ƙarar da ta shigar da kuma yanke hukunci a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.
Cibiyar ta SERAP ta kuma buƙace shi da ya nemi shawarar shari’a daga babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mista Lateef Fagbemi, SAN, kan ko CBN na da hurumin bin doka da oda na ayyukanta ta hanyar dakatar da ƙarin cajin kuɗin amfani da ATM, har sai an yanke hukunci a kan lamarin.
A watan da ya gabata ne SERAP ta shigar da ƙara a kan babban bankin na CBN “a kan gazawar da aka yi wajen sauya ƙarin kuɗin hada-hadar kuzi na ATM da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Shari’ar dai ta biyo bayan sanarwar da babban bankin na CBN ya fitar na cewa cire ATM ɗin da aka yi a wata na’ura mallakar banki amma a wajen harabar reshensa a yanzu za a riƙa biyan N100 duk naira 20,000 da aka cire. Cire ATM a cibiyoyin cefane, filayen jirgin sama ko kuma wuraren ajiyar kuɗi na tsaye, za a biya kuɗin N100 tare da ƙarin kuɗi har zuwa N500.
A cikin buɗaɗɗiyar wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Maris, 2025 mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare, ƙungiyar ta ce: “A umarci CBN ya dakatar da ƙarin kuɗin ATM, wanda zai bai wa babbar kotun tarayya damar sauraren ƙarar.”
SERAP ta ce, “Haka kuma zai yi daidai da ƙa’ida da tsarin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yinwa kwaskwarima).”
A cewar SERAP, “Aiwatar da ƙarin kuɗin ATM a yayin da ake ci gaba da shari’ar a gaban babbar kotun tarayya zai nuna rashin girgima wa ga tsarin shari’a da bin doka da oda.
SERAP ta kuma ce, “CBN ya dakatar da ƙarin kuɗin hada-hadar kuɗi na ATM, sannan ya jira sakamakon ƙarar.”
