Dalilin da ya sa nake fuskantar barazanar kisa – Shugabar NAFDAC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Farfesa Mojisola Adeyeye, Darakta Janar na Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta bayyana cewa tana fuskantar barazanar kisa sakamakon ƙoƙarin da hukumar ta ke yi na tarwatsa manyan cibiyoyin samar da magungunan jabu a Kano, Idumota, Yaba, da Onitsha.

Duk da wannan barazanar, Adeyeye ta jajirce wajen kawar da magungunan jabu a kasuwannin Nijeriya, inda ya yi alƙawarin ba za ta razana ba.

Da take jawabi a Abuja, ta bayyana ƙudurinta na yi wa jama’a hidima, inda ta ce daman can ta yanke shawarar barin rayuwa mai daɗi a Amurka— inda ta rayu tsawon shekaru 37 — ta koma Nijeriya domin ci gaba da aikin hidimta wa al’umma.

“Na dawo gida don yin hidima. Zan iya zama a Amurka, cikin kwanciyar hankali. Amma ina kallon rawar da nake takawa a nan a matsayin manufa,” inji ta.

Ta amince da hatsarin amma ta jaddada cewa barazanar ba za ta hana ita ko ƙungiyarta cika aikinsu na kare lafiyar jama’a ba.

Adeyeye ya kuma bayyana irin hatsarin da jami’an hukumar ta NAFDAC ke fuskanta, inda ya bada labarin wani mummunan hari da aka kaiwa wani jami’i a wani samame da suka kai a Onitsha.

“An yi wa ɗaya daga cikin ma’aikaci na dukan tsiya kuma aka bar shi cikin jini a Onitsha watanni shida da suka wuce. Na taɓa lura da wani rauni a hannun wani ma’aikaci kuma na tambayi abin da ya faru. Ta ce min ta kusa rasa ranta a lokacin da ake dubata,” inji ta.

Duk da ƙalubalen da ake fuskanta, Adeyeye ta sake jaddada aniyarta na ganin ‘yan Nijeriya sun samu lafiyayyun magunguna masu inganci, inda ta bayyana cewa tsoro ba shi da gurbi a aikinta.

By ukarofi