Iƙirarin neman lalata manuniya ce ta raunin Natasha – Sanata Ita-Giwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohuwar sanata a Nijeriya, Florence Ita-Giwa, ta caccaki Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin cin zarafinta, inda ta ce da zarar mata sun zama sanatoci sun fi ƙarfin a nemi yin lalata da su.

Ita-Giwa, wacce sanata ce mai wakiltar Kuros Riba ta Kudu tsakanin 1999 zuwa 2003, yayin da take magana a gidan talabijin na Arise a ranar Talata, Ita-Giwa ta bayar da hujjar cewa, alama ce ta rauni ga ‘yan majalisa mata yin irin wannan iƙirarin.

Ita-Giwa ta ce, “a lokacin da kuka tsaya takara har ku ka isa Majalisar Dattawa, kun wuce matakin rayuwar a nemi lalata da ku. Kowa mataki ɗaya yake a majalisa.”

Da aka tambaye ta ko ya kamata ’yan majalisar mata su yi shiru game da cin zarafi daga abokan aikinsu, Ita-Giwa, wacce tsohuwar mai baiwa Shugaban ƙasa shawara ce, ta dage cewa yin irin waɗannan zarge-zargen nuna rauni ne.

“A wannan matakin na siyasa, idan ka fito ka ce wani yana neman lalata da kai, rauni ne,” inji Ita-Giwa.

By ukarofi