Real Madrid ta nuna matsuwa kan ɗan wasan Bournemouth mai shekara 19 daga Sifaniya, Dean Huijsen, wanda cikin yarjejeniyarsa ake iya biyan fam miliyan 50 domin sayensa ga wata ƙungiya.
Barcelona na duba yiwuwar mallake ɗan wasan Newcastle mai shekara 27 daga Brazil, Bruno Guimaraes, wanda ƙungiyoyin Arsenal da Manchester City ke zawarci.
Dan wasan tsakiya a Bayern Munich da Jamus, Joshua Kimmich mai shekara 30 na son zuwa Arsenal, yayinda ita ma Paris St-Germain ke nuna zawarcinta.
Dan wasan Manchester United da Brazil, Antony mai shekara 25, ya nuna sha’awar cigaba da zama a Real Betis idan yarjejeniyar zaman aronsa ta kawo ƙarshe a ƙungiyar ta La Liga club.
Liɓerpool ta kasance ƙungiya ta baya-bayanan da ke zawarcin ɗan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko mai shekara 21 daga Sloɓenia wanda burinsa ya je Landan, sannan Arsenal da Chelsea na bibbiyarsa.
Tottenham na iya rabuwa da ɗan wasan Mali, Yɓes Bissouma mai shekara 28 a wannan kaka, yayinda take ƙoƙarin sake garambawul a tawagarta.
West Ham ta tuntubi ɗan wasan Roma mai shekara 27 da Ingila, Tammy Abraham, da yanzu haka ke zaman aro a AC Milan.
Newcastle na duba yiwuwar saye ɗan wasan Fiorentina, mai shekara 25 daga Italiya, Moise Kean.
Everton za ta bada damar sake daidatawa kan ɗan wasan Brazil, Richarlison mai shekara 27 daga Tottenham.
Liɓerpool na son ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40.
West Ham na ƙoƙarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka.
Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a Burnley, James Trafford mai shekara 22 ko kuma Joan Garcia mai shekara 23 daga Sifaniya, domin maye gurbin Andre Onana mai shekara 28 na Kamaru.
Real Madrid na son ɗan wasan Liɓerpool mai shekara 25 daga Faransa, Ibrahima Konate.
